News
Ban Koma PDP Don Son Kai Ba – Shekarau
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau a ranar Alhamis ya kare matakinsa na ficewa daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party zuwa jam’iyyar PDP gabanin zaben 2023.
Da yake magana a gidan Talabijin na Channels TV’s Politics Today, Shekarau ya caccaki wadanda suka soki tafiyar sa daga jam’iyyar All Progressives Congress zuwa NNPP da yanzu ya koma PDP cikin shekaru biyar a matsayin alamar rashin da’a a siyasance.
YANZU-YANZU: Atiku ya sauka a Kano domin karɓar Shekarau zuwa PDP
“Da a ce halina ne na yi duk abin da ya dace saboda son raina – ka tambayi kowane talakan Kano; da jama’a ba za su zo tare da mu ba idan da wani abu ne na son kai ko don son rai,” inji Shekarau.
“Duk lokacin da muka tashi, muna da tsari tun daga sashin zuwa unguwa zuwa karamar hukuma, zuwa jiha.
“Siyasar mu ta kasance siyasa ce ta tuntuba, tuntubar juna sosai. Babu wani mataki da na dauka a siyasance ba tare da an gudanar da zaben raba gardama a fadin jihohi ba.”
Shekarau wanda tsohon Ministan Ilimi ne ya ce ya koma PDP ne saboda ba jam’iyyar mutum daya ba ce ba don an yi masa alkawarin wani mukami na siyasa ba.
Ya kuma yi alkawarin cewa PDP za ta lashe jihar Kano a zaben shugaban kasa na badi.
“Mutanen Kano sun amince da mu,” in ji shi. “Ina tabbatar muku da yardar Allah, PDP za ta share kuri’u a Kano, idan ba duka ba, sai mafi rinjaye. Domin na san abin da mutane ke so.”
