Opinion
KADAN DAGA CIKIN DALILAN DA SUKA SA NA DORA LAIFI AKAN GWAMNATIN KANO – Abba Hikima
1. Hanyoyi masu kwalta aka dinga fasawa da izinin gwamnatin Kano ana gida shaguna masu bene.
2. An toshe manyan kofofin shiga kasuwar da dama anyi shaguna da izinin gwamnati. Wanda ta wannan hanyoyi ruwa ke kwarara.
3. Hukumar KNUPDA da kanta ta dinga sayarwa da kananan yan kasuwar teburan karfe masu dauke da hatimin KNUPDA in ban manta ba akan kudi N80,000 duk daya.a wasu layikan ma irin su Bajallabe layi 2 ko 3 aka yi wadannan tebura akan tsakiyar titi.
4. Ni da kaida lokacin muna tattara hujjojin zuwa kotu mun auna titi mai fadin kafa 60 amma ya dawo kafa 8. Ko mota daya baza ta iya wucewa ba. Saboda son rai mutane wadanda gwamnati ta bari.
5. Da izini ko sahhalewar hukumomin tsara birane da kula da tituna ake duk abun da ake yi saboda aikin su ne basu yi. Ba inda mutune suke yin dai dai a kan kansu in ba’a auwatar da doka.
6. Yan kasuwa da dama sun magantu akan wannan amma aka ki yin komai. Hasali ma a karkashin shugabancin Alh Balarabe Tatari har kotu muka shigar da gwamnatin Kano amma daga karshe aka yi makarkashiya aka cire shi daga shugabancin saboda yaki bada kai.
Sai an samu matsala sai ace Allah ne ya kawo.
Copy Abba Hikima Facebook
