News
Ruwan sama ya kashe mutum biyar, ya lalata gida 3,813 a Katsina
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Mutum biyar ne suka mutu sannan gida 3,813 suka lalace sakamakon wani ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a kananan hukumomi 13 da ke Jihar Katsina a Najeriya.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Jihar ce ta bayyana haka ranar Litinin din nan.
Mutum 8 Sun Nitse A Ruwa A Jigawa
A yayin da yake hira da manema labarai, kakakin hukumar, Malam Umar Muhammad, ya ce mutum uku sun mutu a karamar hukumar Kankara yayin da mutum biyu suka rasu a Mai’adua.
Ya bayyana cewa gwamnatin Jihar tana yin dukkan abin da ya kamata domin ambaliyar ruwa ba ta auku a jihar ba, yana mai cewa an kafa kwamitin gaggawa wajen ganin ba a fuskanci barkewar amai da gudawa ba.
Ya ce: “A Kankara, gidaje 176 sun rushe, a Danja kuma gida je 125 suka lalace, sai kuma Kankia inda gidaje 86 suka rushe, yayin da a birnin Katsina gidaje 620 suka lalace, Musawa 482, Batagarawa 361, Kusada 311 yayin da Sabuwa gidaje 111 suka rushe.
“A Zango, ruwan saman ya lalata gidaje 105, a Batsari, ya rusa gidaje 443, a Funtua gidaje 258 sun rushe, a Safana gidaje 581 sai kuma Ingawa kusan gidaje 154 suka rushe.
“Kazalika gidaje 176 sun rushe yayin da mutum uku suka rasu a ibtila’in a Kankara yayin da gidaje 154 suka lalace a Ingawa.”
