Connect with us

News

An Kama Malamin Da Ya Yi Wa Daliba ’Yar Shekara 7 Fyade A Bauchi

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kamo wani malamin makaranta mai shekaru 25 da ake zargi da yi wa dalibarsa mai shekaru bakwai fyade.

 

Advertisement

Kakakin rundunar, SP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana wa Aminiya cewa wanda ake zargin ya ja dalibar ne zuwa ofishinsa da ke makarantar Royal Science Academy a jihar, inda ya yi mata fyade.

An kama matsafa shida kan yunkurin kashe basarake a Ogun

Advertisement

 

Wakil ya ce wasu karin mutane bakwai da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar sun shiga hannu.

Advertisement

 

“Mun samu labarin cewa wani malami mai suna Sirajo Ahmad da ke koyarwa a makarantar Royal Scence ya yi wa yarinya fyade.

Advertisement

 

“Bayan shi kuma akwai wani mai mai shekaru 35 da ke sayar da Askirim a unguwar Bacas, wanda shi ma ya yi wa wani yaro mai shekaru 12 fyade.

Advertisement

 

“Binciken da muka gudanar ya nuna mutumin ya sayi ruwan leda ne a wurin yaron, daga bisani ya ja shi wani shago ya yi masa fyade”, a cewar kakakin.

Advertisement

 

Ya ci gaba da cewa, a ranar Litinin ma ofishin rundunar da ke Tafawa Balewa a Bauchin, ya kamo wani ikirarin sayar da magungunan gargajiya wanda ya yi wa wata mata fyade.

Advertisement

 

“Wanda ake zargin ya yi wa matar fyade ne bayan ta kai masa ’yarta mara lafiya don ya ba ta magani.

Advertisement

 

“Daga nan ne ya shaka mata maganin barci, sannan ya yi mata aika-aikar”, in ji Wakil.

Advertisement

 

Kazalika, ya ce za a gabatar da dukkanin wadanda ake zargin a gaban Kotu, domin su girbi abin da suka shuka.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending