Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wani matashi da bindiga a unguwar Gadon Kaya dake cikin birnin Kano.
Mai magana da yawun rundunar,SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun kama matashin mai shekaru 25 da haihuwa, mai suna Nasir Kabir sakamakon yunkurin kashe mahaifinsa.
An Kama Malamin Da Ya Yi Wa Daliba ’Yar Shekara 7 Fyade A Bauchi
Nasir Kabir ya bayyanawa ‘yan sanda abinda yake niyyar yi da bindigar.
Ya ce, sau uku yana kokarin kashe mahaifinsa don ya gaje dukiyarsa kuma yaji dadi kamar yadda abokansa ke yi, amma hakan ya citura.
Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa, matashin ya fara shawaran kashe mahaifin ne lokacin da wani mahaifin abokinsa ya rasu a 2018 kuma ya ga yadda abokin ya samu kudin gado da yawa har ya sayi Babur