Connect with us

News

Fashewar Iskar Gas Ta Raunata 5, Shaguna 17, Gidaje 5 A Jigawa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya NSCDC a jihar Jigawa ta bayyana a ranar Talata cewa mutane biyar sun jikkata sakamakon fashewar iskar gas da ake kyautata zaton fasa kwaurinta ne a karamar hukumar Babura ta jihar.

Advertisement

 

Kakakin hukumar NSCDC, CSC Adamu Shehu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai  NAN a Dutse, ya kara da cewa fashewar ta kuma lalata shaguna da gidaje.

Advertisement

 

Osinbajo ya sauka a Nairobi domin bikin rantsar da sabon shugaban ƙasar Kenya, Ruto

Advertisement

Kazalika, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) a jihar, DSP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin.

 

Advertisement

Ya ce shaguna 17 da gidaje 5 ne suka lalace sakamakon gobarar da fashewar ta haddasa.

 

Advertisement

Kakakin hukumar NSCDC, Shehu, a cikin asusun sa, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 9:00 na dare, bayan da jami’an tsaro da suka tsaya da bincike a yankin suka yi kaca-kaca da wata motar daukar kaya mai dauke da bututun iskar gas guda 25.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Ya yi zargin cewa direban motar ya ki tsayawa dalilin da ya sa jami’an suka bi su, wanda hakan ya sa daya daga cikin silinda ya fado daga motar kuma nan take ya kama wuta.

Advertisement

 

Kakakin ya kara da cewa motar ta taho ne daga garin Tinkim da ke karamar hukumar Magarya ta Jamhuriyar Nijar kuma ta nufi karamar hukumar Hadejia ta jihar Jigawa.

Advertisement

 

Ya ce a halin yanzu wadanda abin ya shafa suna karbar magani a babban asibitin Babura.

Advertisement

 

Hakazalika, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO) a jihar, DSP Lawan Shiisu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Advertisement

 

Karanta Haka kuma: Ingantattun PHCs: Solacebase tana jan hankalin masu ruwa da tsaki a harkar lafiya a Kwara

Advertisement

 

Shiisu ya ce, wata tawagar jami’an hukumar hana fasa kwabri ta Najeriya ta kwastam mai lamba 12 ne ke bin motar a yayin da take jigilar iskar gas daga jamhuriyar Nijar.

Advertisement

 

Ya kara da cewa shaguna 17 da gidaje biyar ne suka lalace sakamakon gobarar da fashewar ta haddasa

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Solacebase

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending