Kauyuka da dama, da hanyoyi da gonaki, har ma gadoji ne ambaliyar ruwa ta yi awon-gaba da su a wasu yankunan jihar Yobe da ke maso maso gabashin Najeriya.
Wani babban jami’i a kananan bankunan bayar da rance na Jihar, Sheriff Almuhajir ne ya wallafa hotunan irin barnar da ambaliyar ta yi a shafinsa na Facebook ranar Laraba.
Gwamnatin Kano Ta Musanta Siyar Da Harabar Wasu Kotunan Jihar
Ya yi zargin cewa bala’in da suke ciki a Yobe na faruwa ne saboda ambaliya a dam din Tiga da ya fito daga Kano ya bi Hadejiya a jihar Jigawa, daga nan ya dangana da Nguru da Gashua a jihar ta Yobe.
A cewarsa ya kamata a ce masu zuba jari a harkar noma su yi amfani da damar isasshen ruwan da ke yankin don jama’a su amfana a kuma kawar da bala’in ambaliyar.
Yobe ta shiga sahun sauran jihohin Arewacin Najeriya da suka hada da Jigawa, da Kano, da Bauchi, da Adamawa, da ambaliya ta yi sanadin mutuwar mutane da dama, da kuma rusa dubban gidaje.
