News
Gwamnatin Kano Ta Musanta Siyar Da Harabar Wasu Kotunan Jihar
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban kwamitin tattaunawa da gyaran wasu wurare mallakar gwamnatin jihar Kano, Barista Musa Abdullahi Lawan, ya bayyana ikirarin cewa gwamnatin Kano ta sayar da wasu kotunan shari’a ga wasu mutane da cewa labarin ƙanzon kurege ne.
Shugaban wanda kuma shi ne Babban Lauyan gwamnatin Jihar Kano kuma Kwamishinan Shari’a ya mayar da martani ne kan ikirarin da wasu Lauyoyin Jihar Kano, Barista Sanusi Umar da Barista Usman Imam da Kwamared Bello Basi suka yi, inda suka garzaya Babbar Kotun Jihar da ke neman ta hana Gwamnatin Jihar, daukar wani kan ginin da harabar kotuna.
Kante da Mendy ba za su buga wa Chelsea gasar Zakarun Turai ba
Kotunan da abin ya shafa sun hada da, Kotun Shari’a ta Gidan Maitasine, da Yan Awaki, da Kotun Shari’a ta Yan Alluna, da Kotun Shari’a ta Shahuci, da Kotun Shari’a ta Goron Dutse, Sauran sun hada da Shari’a Court Kasuwar Kurmi, da Kotun Shari’a ta Filin Hockey.
Babban Lauyan ya ce akwai kuskuren bayyana gaskiya dangane da ikirarin da masu shigar da kara uku suka yi.
A wani labarin kuma: Rundunar Yan Sanda Ta Karɓi Ƙorafe Ƙorafen Jama’a 431 Kan Jami’anta
Rundunar Yan sanda ta kasa tace ta samu korafe-korafe sama da 431 daga ‘yan kasarnan, kan jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya tsakanin watan Yuli zuwa 5 ga Satumba, 2022.
Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa daga cikin wadancan adadi an warware korafe-korafe 304 tare da yanke hukunci 81 ga jami’an ‘yan sanda da suka yi kuskure.
Wadannan suna kunshe ne a cikin wata takarda da ministan harkokin ‘yan sanda, Maigari Dingyadi ya shirya, yayin da yake bayyana kokarin ma’aikatarsa wajen tabbatar da da’a a tsakanin jami’an ‘yan sanda
