News
Kotu ta umarci INEC ta amince da Akpabio a matsayin dan takarar sanata a APC
Advertisements

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja babbar birnin Najeriya ta umarci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar da ta amince tare da wallafa sunan Godswill Akpabio a matsayin dan takarar kujerar sanata mai wakiltar yankin Akwa Ibom ta arewa maso yamma a karkashin jam’iyyar APC.
Advertisements
Advertisements
Jam’iyyar APC dai ta wallafa sunayen Shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawan da tsohon ministan Niger Delta Godswill Akpabio, da kuma gwamnan jihar Ebonyi Dave Umahi, a matsayin ‘yan takarar majalisar dattawa a karkashin jam’iyyar
To sai dai hukumar zaben kasar ta cire sunayensu daga cikin jerin sunayen ‘yan takara da ta wallafa
Advertisements
