News
ICPC ta bankado almundahar N2.8 na ayyukan mazabu cikin shekara uku
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar da ke yaki da cin hanci da almundahanar kudade ta ICPC a Najeriya ta ce ta gano ayyukan mazabu da aka karkatar a fadin kasar da kudinsu ya kai Naira biliyan 2.8
Hukumar ta ce ta gano hakan ne ta hanyar wani kwamiti da ta kafa don bin diddigin ayyukan mazabu a fadin kasar.
Ba za mu ƙara wa’adin da sakamakon jarrabawar JAMB ta ke yi ya dena amfani ba
Wanda ya gano ayyukan mazabu kusan 2,444 da aka karkatar da kudinsu tsakanin shekarar 2019 zuwa 2021.
Yayin da yake yake gabatar da takaitaccen kundin binciken hukumar a birnin Legas, daraktan gudanarwa na hukumar Akeem Lawal, ya ce a karon farko an gano ayyukan mazabu 524 a jihohi 12 da babban birnin tarayya a shekarar 2019.
Sannan kuma a karo na biyu, kwamitin bin diddigin ya gano ayyukan mazabu 822 a jihohi 16 a shekarar 2020,
Haka kuma a karo na uku na bin diddigin an zakulo ayyukan mazabu 1,098 a jihohi 17 hade da Abuja babban birnin kasar.
