News
Ba za mu ƙara wa’adin da sakamakon jarrabawar JAMB ta ke yi ya dena amfani ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Farfesa Ishaq Oloyede, Babban Sakataren Hukumar Shirya Jarrabawar shiga shiga Makarantun Gaba da Sakandire, JAMB, ya koka kan kiran da aka yi na tsawaita ingancin sakamakon JAMB sama da shekara guda.
Oloyede ya bayyana haka ne a wani zama da kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kudi na majalisar wakilai ta yi kan tsarin kashe kudade na matsakaicin zango na shekarar 2023-2025/Fiscal Strategy Paper, MTEF/FSP.
An Kashe ’Yan Bindiga Suna Tsaka Da Rabon Kudin Fansa
Ya ce masu kira da a tsawaita wa’adin da sakamakon JAMB ke yi ya dena amfani sakamakon ba su yi la’akari da yanayi da kuma abubuwa da dama da ke tattare da hakan.
Wani da ya yi jarrabawarmu a bana ya ci 240 yana son karanta fannin ilimin kimiyyar lafiya, ya san idan ba maki 280 ba, ba zai iya samun gurbin shiga makaranta ba, sai ka ce masa kada ya yi jarrabawa, duk da ya kai shekara 10, ba zai iya ba saboda, wasu sabbin rukunin ɗalibai da za su yi jarabawa kuma su sami maki mafi girma kuma mutumin zai kasance a inda yake.
“Ga wadanda suka karanta fannin ilimi, muna da jarabawa iri biyu da za ku tantance maki; za ku ce kashi 50 cikin 100 na bashi, duk wanda ya samu ya tafi. Kuma duk wanda bai yi ba, ya gaza.
