News
Ganduje ya amince da biyan miliyan 304 na alawus-alawus ga malaman jami’ar gwamnatin Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Jihar Kano ta amince da biyan Naira miliyan 304 a matsayin alawus-alawus ga ma’aikata 287 na ɓangaren koyarwa na jami’ar Yusuf Maitama Sule, YMSU da suka cancanta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya fitar a Kano a yau Juma’a.
Kotu ta soke zaben fidda gwanin gwamna a Zamfara
Ya bayyana cewa an ba da wannan amincewar ne a taron majalisar zartarwa na jihar na mako-mako.
Muhammad ya ƙara da cewa za a rika biyan kudaden alawus-alawus ɗin ma’aikatan ne daki-daki a kowane wata daga watan Oktoba.
“Za a biya Naira miliyan 297 ga ma’aikatan fannin koyarwa da aka tantance, yayin da aka kiyasta Naira miliyan 6.5 don a biya sauran ma’aikata ilimi 10 da a ka cire sunayensu bisa kuskure a biyan kuɗin da ya gabata.
“Majalisar ta kuma amince da sakin Naira miliyan 82.1 ga YMSU domin samar da ayyukan gyaran makaranta kai tsaye da kuma samar da kayan aiki a tsangayar kimiyya,” inji shi.
Majalisar ta kuma amince da Naira miliyan 84.9 ga Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jiha da ke Wudil.
Kuɗin don biyan ɗalibai ne da su ka je shirin sanin makamar aiki a masana’antu, SIWES, da kuma alawus-alawus na zuwa saba’in makamar aiki koyarwa na zango biyu na 2019/2020 da 2021/2022 ga ma’aikatan ilimi da suka cancanta.
