Business
Masana Sun Bayyana Abubuwan Da Za Su Sa Abinci Ya Kara Tsada A Bana
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hasasahe na nuna da cewa, akwai yiwuwar abinci ya kara tsada a bana. A cewar wasu ƙwararru, dalilai da yawa suka sa ake wannan hasasahen.
Dalili na farko da masanan suka bayyana shi ne, ambaliyar ruwa a wadansu jihohin Nijeriya, wanda hakan zai sa, a yi asarar amfani mai yawa a wasu jihohin da ke kasar nan.
Yanzu haka maganar nan da ake yi wannan hasashe na masama ya tabbata a wasu jihohin Arewacin Nijeriya, irin su, Sakkwato da Nasawa da kuma wasu jihohin Arewacin Nijeriya.
Wata Mace Ta Haifi ’Yan Tara A Haihuwa Daya A Mali
Wani abu da masanan suka bayyana a matsayin abin fargaba, na abin da zai sa abinci ya yi tashin gwauron zabo shi ne, fargabar da manoman ke yi na rashin tsaro, wanda ya sa musamman manyan manoma sun kaurace wa noman a bana, wanda hakan ta rage yawan noman da ake yi, hakan kuma na nuna cewa, akwai yiwuwar abinci ya yi tsada a bana.
Baya ga tsadar takin zamanin, manyan manoma sun koka da tsarar man da za a zuba wa inji domin ban-euwa lokacin noman rayi da kuma tsadar iri.
Wani babban kalubalen kuma shine, tsadar aikin, musamman da yake wadanda ake dauka aikin a halin yanzu na fargabar shiga gonakin domin yin aikin sabida barazanar tsaro.
Manoma da dama sun tabbatar da yadda a yanzu haka dole ta sa suka bar zuwa gonakin nasu saboda yadda ƴan bindiga suke cin karen su ba babbaka inda suke kame manoman wani lokacin kuma suna kashe su.
Wadannan abubuwa na daga cikin abubuwan da ake hasashen cewa, za su sa abinci ya yi tsada a bana.
Wani abu da ya rage yawan noman da ake a bana shi ne, yadda wasu gwamnatocin jihohi suka tsame hannunsu dangane da tallafin da suke bai wa manoman.
Haka kuma, rahotanni sun tabbatar da cewa, akwai wata cuta da ta bulla musamman a wasu sassa na jihar wassa ke kama masara da dawa, wanda wasu manoman da yawa su bayyana wannan cutar a matsayin babbar barzana ga amfanin gonar na bana.
Wadannan abubuwa da aka ambata na daga cikin abubuwan da suka sa, ake hasashen cewa, akwai yiwuwar abinci a bana ya kara tsada.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
