Business
NNPC ta tabbatar da ba za a yi wahalar man fetur na al’ada a watan Disamba
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH
Kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya ce Nijeriya ba za ta fuskanci karancin man fetur ɗin nan na al’ada a watan Disamba da kuma bayan shi ba, la’akari da tanadin isasshen albarkatun man feturin da Kamfanin ya yi.
Babban jami’in kula da harkokin kudi na kamfanin Umar Ajia ne ya bayyana hakan a lokacin da ya bayyana a gaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai kan tsarin tallafin man fetur a Najeriya.
Ajia ya bayyana cewa kamfanin ya samar da isassun matakan dakile matsalar karancin man fetur a kasar, ko da bayan babban zaben 2023.
Shugaban Kwamitin kulada sarrafa albarkatun man fetir Ibrahim Al-Mustapha daga jihar Sokoto ya ce akwai bukatar a kara yin nazari a kan farashin man fetur a Najeriya, daidai da farashin mai a duniya.
Al-Mustapha ya ce ana sayar da man fetur a kan Naira 536 a kowace lita a jamhuriyar Nijar, sai kuma Naira 577 a Mali da kuma Naira 389 a Jamhuriyar Benin.
Ajia ya ce man fetur da ake baiwa ‘yan Najeriya tallafin man fetur ana jigilar su zuwa kasashe makwabta.
Ya ce a sakamakon dagulewar al’amuran iyakokin, hakan kan sanya zirarewar tallafin man fetur da ‘yan Najeriya za su sha da sauran kasashe makwabta.
“Idan kuna da Naira miliyan 5, za ku iya tsallaka kan iyaka da manyan motoci da man fetur, muna da iyaka; eh muna da kwastam amma duk tamkar rariya,” inji shi.
Kwamitin ya shiga wani zaman sirri don kara tattaunawa kan lamarin.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
