Connect with us

News

Za mu mutunta sojojin Russia idan su ka miƙa wuya — Zelensky

Published

on

Zelensky

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ce za su rike sojojin Rasha – da suka mika wuya – cikin ‘mutuntawa’

A wani jawabi da ya gabatar cikin dare Mista Zelensky ya yi kira ga dakarun Rasha da su mika wuya ga kasar Ukraine ko su san inda dare ya yi musu.

Advertisement

Wannan na zuwa ne bayan da shugaban Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan dokar hukunta sojojin kasar wadanda suka gudu daga fagen daga ko suka ki bin umarni, inda dokar ta tanadi daurin shekara 10 a gidan yari kan wadanda suka aikita laifin..

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Rasha OVD-Info, ta bayar da rahoton cewa an kama mutum 700 a ranar Asabar, bayan da aka tsare fiye mutum 1,000 a farkon mako.

Advertisement

A karkashin dokar kasar Rasha gangamin da bai samu sahalewar hukumomi ba babban laifi ne.

Yayin da yake jawabi, shugaba Zelensky na Ukraine ya umarci sojojin Rasha da su mika wuya ka Ukraine domin kauce wa tuhumar laifin yaki bayan karewar yakin.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending