Connect with us

Business

Afirka ta Kudu ta gargadi MTN kan yaudarar masu sayen datar kwana 1

Published

on

MTN

DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH

Hukuma ta gargadi kamfanin wayar salula mafi girma a Afirka saboda yaudarar abokan huldarsa game da sayar musu da kunshin data na kwana 1.

A yanzu kunshin datar MTN ta kwana 1 ba ta karewa bayan awa 24, maimakon haka tana karewa ne cikin tsakar daren ranar da mutum ya sayi datar, ba tare da la’akari da komai kurewar lokacin da aka saya ba.

Ofishin kula da Harkokin Tallace-tallace na Afirka ta Kudu ya bayyana shirin a matsayin “mai fuska biyu don haka akwai yaudara a cikinsa”, abin da ya sa hukumar ta nemi MTN a wannan mako ya janye tallace-tallacen da yake yi na kunshin datar.

Wata kafar yada labarai mai suna Business Insider South Africa ce ta yada hoton tallar kunshin datar na MTN, lamarin da ya haifar da korafe-korafe.

BBC

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending