Business
Kamfanonin Waya Za Su Yanke Hulda Da Bankuna Saboda Taurin Bashi
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kamfanonin sadarwa sun yi barazanar yanke hulda da bankunan Najeriya da kuma sauran kamfanonin hada-hadar kudi saboda taurin bashi.
Barazanar daukar wannan mataki ya fito ne daga Shugaban Kungiyar Kamfanonin Sadarwa ta Najeriya (ALTON), Injiniya Gbenga Adebayo, a wani jawabi da ya yi a taron kungiyar masu bayar da rahotanin kan al’amuran sadarwa ta kasa (NITRA) a jihar Lagos.
Gwamnatin Tanzania ta haramta wa bankuna cajin kwastamomi kuɗin taransfa
Injinya Adebayo ya ce bankuna suna cire kudinsu daga kwastomininsu amma sai su ki biyan kamfanonin sadarwa nasu hakkin.
“Haka ba za ta yiwu ba, domin banki ba zai bi ka bashin kwabo ba ya kuma bar ka ka sarara, sai ka biya, amma yanzu mu yanzu ga shi muna bin su bashi amma sun ki biya,” inji Adebayo.
Sannan ya ce, idtan suka yanke huldarsu da bankunan, mutane ba za su iya aikewa da kudi ko karbarsu ba ta hanyoyin zamani kamar waya da suransu.
Adebayo ya kuma ce an kusa kai wa ga hakan, domin kamfanonin sadarwar ba su da zabi idan bankunan su ka ci gaba da kin biyan bashi face su dauki matakin.
Banki
Kamfanonin sadarwa
kamfanonin waya
Daily TRUST
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Cafke Mai Safarar Makamai, Sun Kwato Harsasai 637 A Kaduna
-
News7 days ago
Jami’an NSCDC Sun Cafke Mutane Biyu Da Saniyar Da Ake Zargin Ta Sata Ce A Kano
-
News4 days ago
2027: INEC Ta Tabbatar Da Ibrahim Ali Amin Little A Matsayin Ɗan Takarar Gwamnan Kano A Jam’iyyar ADC
