Connect with us

News

An shiga farautar maharan da suka kashe sojojin Najeriya biyar a Anambra

Published

on

Sojoji

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Dakarun tsaro na can suna neman ‘yan bindigar da suka kashe sojojin Najeriya a kalla biyar cikin jihar Anambra, da ke kudancin kasar.

Zuwa yanzu babu wata kungiya da ta fito ta ce ita ce ke da alhakin kai wannan hari na ranar Laraba a Umunze kusa da fitacciyar kasuwar Nkwo.

Sai dai hukumomi a kasar sun sha zargin kungiyar IPOB da kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin gwamnati da jami’an tsaro a Anambra da ma sauran jihohin kudu maso kudu.

Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya yi tur da wannan kisan gilla.

Ya kuma ce dole ne a farauto wadanda suka aikata mummunan aiki tare da hukunta su.

Advertisement

BBC

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending