News
Kotu ta soke zaɓen A’isha Binani
DAGA MUSLIM YUNUS ABDULLAH
Babbar kotun tarayya da ke zaman ta a Yola ta soke zaɓen fitar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Adamawa, wanda Sanata A’isha Binani ta lashe.
A hukuncin da ta yanke, mai shari’a A.M Anka ya buƙaci Aisha Binani ta daina bayyana kanta a matsayin ƴar takarar gwamna a zaɓen gwamna na shekara ta 2023.
Kotun ta ce zaɓen ya zama haramtacce saboda aringizon ƙuri’a da kuma kawo wakilai daga ƙaramar hukumar Lamurde, inda ba a gudanar da zaɓen cikin gida na jam’iyyar ba.
Tsohon shugaban Hukumar Yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa (EFCC) Mallam Nuhu Ribadu ne ya shigar da ƙarar, inda ya buƙaci kotu ta soke zaɓen, wanda aka gudanar a watan Maris.
Inda ya yi zargin an yi aringizon ƙuri’u, da sayen ƙuri’a da kuma bai wa daliget cin hanci.
Yanzu haka kotun ta ce jam’iyyar All Progressive Party ba ta da ɗan takarar gwamna a jihar ta Adamawa a zaben shekara ta 2023.
BBC HAUSA
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
