News
Na Ji Daɗi Yadda Musulmi Suka Fara Rufe Asusunsu Na Bankin Polaris— Bulama Bukarti
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Fitaccen lauyan nan mai rajin kare haƙƙin bil’adama, Bulama Bukarti, ya ce ya ji daɗi bisa yadda Musulmi suke fara rufe asusunsu na Bankin Polaris saboda tsarin bankin na hana ma’aikatansu Musulmi zuwa Sallar Juma’a.
Bukarti ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Juma’a.
Kotu ta soke zaɓen A’isha Binani
Labarai24 dai ta kawo rahoton yadda Musulmi ma’aikatan bankin na Polaris suka koka bisa yadda bankin yake hana su zuwa Sallar Juma’a.
Sai dai bankin a wani martani da ya mayar ya ce Najeriya ƙasa ce da ba ruwanta da addini, kuma shi ba shi da tsarin hana kowa daga cikin ma’aikatansa yin addinin da ya zaɓa wa kansa.
“Na ji daɗin karantawa cewa Musulmai sun fara tururuwar rufe asusunsu na Bakin Polaris saboda tsarinsu na hana ma’aikatansu Musulmai zuwa Sallar Jumu’ah. Ina kira ga dukkan Musulmai su kwashe kuɗinsu, su rufe asusunsu daga wannan bankin idan ba su gaggauta janye wannan tsinennen tsari nasu ba. Nima da ina da shi da tuni na garƙame shi”, in ji Bukarti.
LABARAI 24
