Sports
Gasar Kofin Duniya: Fiye da mutum miliyan 1.5 ne suka nemi tikitin gasar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kasar Qatar ta ce kawo yanzu fiye da mutum miliyan 1.5 ne suka nuna bukatarsu ta sayen tikitin kallon gasar Kofin Duniya da kasar za ta karbi bakunci, wacce za a fara ranar 20 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Shugaban kwamitin sayar da tikitin kallon gasar Saad Al-Suwaidi, ya ce kawo yanzu mutane kusan miliyan 1.7 ne suka bayyana sha’awarsu ta sayen tikitin, wanda zai zama Biza, da kuma tikitin shiga filin wasa, da kuma tikikin zirga-zirga a cikin kasar lokacin gasar.
Mutum 11 sun mutu a hatsarin mota a Bauchi
Duka masu sha’awar shiga Qatar dole su mallaki tikitin domin shiga kasar daga ranar daya ga watan Nuwamba, ko suna da niyyar kallon wasa ko kuma ba su da shi.
Kasar ta ce tana sa ran samun baki fiye da miliyan daya, tare da dubban ‘yan kallo daga cikin kasar.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
