Sports
An kara tsare Greenwood na Man United
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
An kara kama dan wasan Manchester United, Mason Greenwood, saboda ya karya dokar da aka bayar da shi beli.
Mai shekara 21, ana zarginsa da aikata fyade da cin zarafi a watan Janairu.
Ɗalibin da ya koma sayar da abinci sabo da yajin aikin ASUU ya rasu
Ana kuma yi masa tambayoyi kan ikirarin cewar zai yi kisa.
Greenwood, wanda ya yi wa tawagar kwallon kafa ta Ingila wasa daya, ba a fara sauraren tuhumar laifin da ya aikata ba, wanda aka bayar da shi beli cikin watan Yuni.
BBC ta fahimci cewar an kara tsare dan wasan United a gidansa da ke Bowdon, Greater Manchester.
Tuni kungiyar Old Trafford ta dakatar da dan wasan daga atisaye har sai an kammala bincike.
Nike ta soke kwantiragin da ta kulla da shi, sannan Electronic Arts ta fitar da shi daga ‘yan kwallon Fifa 22 game.
BBC
