Sports
Ronaldo ya dawo atisaye bayan hukuncin da Ten Hag ya yi masa
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dan wasan gaban Manchester United Cristiano Ronaldo ya koma atisaye tare da sauran abokan wasansa na kungiyar, bayan hukuncin da Erik ten Hag ya yi masa.
A makon da ya gabata ne kocin ya nemi ya koma atisaye shi kadai, a wani bangare na jan kunnen da aka yi masa.
Hisbah ta kama kwalabe 5,800 na barasa a Kano
Ronaldo mai shekara 37, ya ki shiga wasan da United da ta buga da Tottenham a ranar Larabar da ta gabata saboda an ajiye shi a benci, sannan kuma aka ki amfani da shi a wasan da Manchester ta yi 1-1 da Chelsea.
Ten Hag ya ce bayan wannan hukunci ba wanda za a kara yi masa.
An gano cewa Ronaldo da Ten Hag sun tattauna a cikin wannan kwanakin.
Advertisements
