News
Faɗakarwar Ta’addanci: IGP Ya Bayar Da Lambobin Gaggawa A Duk faɗin ƙasar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar nan, Usman Baba, a daren Alhamis din nan ya fitar da lambobin gaggawa a duk fadin kasar da nufin dakile duk wani hari da ‘yan ta’adda za su kai musu.
Baba ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya na aiki tare da hadin gwiwar sauran jami’an tsaro, domin tabbatar da tsaron dukkanin mazauna kasar.
Yadda Aka Fatattaki Barcelona Daga Gasar Zakarun Turai
Jaridar indaranka ta rawaito cewa, Babban dan sandan ya kuma ci gaba da cewa babu wani hari da ke shirin kai wa babban birnin kasar kamar yadda Amurka ta yi.
Yadda Aka Fatattaki Barcelona Daga Gasar Zakarun Turai
IGP din ya jaddada hakan ne yayin da ya bukaci daukacin manajojin ‘yan sanda masu kula da umarni da tsare-tsare a cikin kasar nan da su karfafa tsaro a yankunansu, musamman a babban birnin tarayya Abuja.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun rundunar, Olumuyiwa Adejobi, IGP din ya kuma ba da umarnin a kunna dukkan lambobin gaggawa a fadin kasar nan tare da cikakken karfin da za a iya mayar da martani cikin gaggawa 24/7.
Majiyar jaridar indaranka ta bada rahoton cewa Adejobi ya ce, rundunar ‘yan sandan ta kuma bayar da umarnin cewa jami’an da ke yaki da masu fada a ji su kasance cikin shirin ko ta kwana domin bayar da amsa idan an samu lamuran gaggawa da kuma kiran gaggawa.
Sanarwar ta kara da cewa, “an yi kira ga mazauna babban birnin tarayya Abuja da su sanya ido tare da kai rahoto ga ‘yan sanda ta layukan gaggawa kamar haka: 08032003913, da 08061581938, da 07057337653, da kuma 0802894083.”
Duk da haka, IGP ya kawar da fargabar mazauna babban birnin tarayya, ya kuma gargade su da su ci gaba da gudanar da sana’o’insu na halal da zamantakewar al’umma, yana mai cewa, dukkan hannaye suna kan hanyar dakile duk wata barazana ta tsaro a cikin gari tare da amsa kiran gaggawa cikin gaggawa.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Baba ya nanata kudurin rundunar ‘yan sandan Najeriya na kawar da duk wata barazana, da kuma kare rayuka da dukiyoyin
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
