Connect with us

News

Mutum 14 Sun Rasu, Gidaje 50 Sun Salwanta A Ambaliyar Gombe

Published

on

Ambaliyar ruwa

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Gombe SEMA ta ce ambaliyar ruwa a bana an janyo asarar rayuka 14 da gidaje sama da 50, tare da shafar kimanin mutane 600 a fadin jihar.

Advertisement

 

Darakta a hukumar ta SEMA kuma mai kula da bada agajin gaggawa, Mihammad Garba, ne ya bayyana cewa ambaliyar tafi shafar kananan hukumomi 7 cikin 11 da ke jihar.

Advertisement

An tafka muhawara tsakanin masu takarar kujerar gwamna a Kano

Aminiya ta rawaito cewa Muhammad Garba, ya ce ambaliyar ta fi shafar kananan hukumomin Akko da Yamaltu Deba da Kwami da Dukku da Kaltungo da kuma Shongom.

Advertisement

 

Sai dai a cewarsa, duk da karamar hukumar Funakaye ba ta cikin kananan hukumomin da ake da rahoton samun ambaliyar, sai gashi a ranar 29 ga watan Yuli an samu ambaliya da ta halaka rayuka 14 da gidaje fiye da 50 da ta shafi magidanta fiye da 600 inda ruwa ya malale garin Bagoja da wasu makwabtan ta baki daya.

Advertisement

 

Ya ce a lokacin da ambaliyar ta faru, sun sanar da gwamnatin jihar inda nan take gwamnan, duk da baya gari, ya umarci ma’aikatar kula da muhalli, suka hadu da SEMA suka je garin suka duba sannan suka bada tallafi.

Advertisement

 

Muhammad Garba, ya ce sun bai wa al’ummar da Aambaliyar ta shafa tallafin kayan abinci da na aikin gida da kuma magunguna.

Advertisement

 

Daga nan sai ya ja hankalin jama’a da cewa su dinga amfani da fadakarwar da ake musu na daukar matakan kariya kafin saukar damina kamar da sa bishiya da sauransu don samun saukin ambaliya.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending