Connect with us

News

Darajar Naira ta yi faɗuwa mafi muni bayan sanar da shirin sauya fasalin kudin Nijeriya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Farashin takardar kudi ta dalar Amurka a Najeriya ya kai kololuwa a kasuwannin musayar kudaden ketare a Najeriya, inda a safiyar yau talata aka rika sauya duk dala daya kan naira 815 zuwa 818, lamarin da ke nuna yadda kudin na Naira ke ci gaba da rasa daraja.

Advertisement

RFi ta rawaito cewa wani bincike ya nuna cewa tun bayan yunkurin babban bankin kasar CBN na sauya fasalin wasu daga cikin takardar kudin Najeriyar ne, aka fara ganin rububin sayen takardar kudin ta dala a kasuwanni, wanda bayanai ke cewa mutanen da ke makare da kudi a ajje suke saurin sayen dalar don kaucewa fuskantar asara.

Kasuwannin musaya na bayan fage dai a yau talata sun wayi gari da karancin dala baki daya lamarin da ya sa rashin daidaituwar farashin kudin na Amurka, dai dai lokacin da sabbin kudin Najeriyar ke shirin fitowa a ranar 15 ga watan Disamba mai zuwa.

Advertisement

A makon jiya ne CBN ya sanar da sake faduwar darajar Naira zuwa 765 kan duk dala guda wanda ke nuna faduwar naira 53 cikin kwanaki 5 mafi kololuwar koma baya da Najeriya ta taba gani a tarihi.

Sabon farashin dalar na CBN ya sanya hauhawar farashin dalar a kasuwannin bayan fage tun gabanin yau talata da aka tashi da ƙamfar ta.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending