Connect with us

News

Hukumar NiMet Ta Yi Hasashen Samun Kwalleliyar Rana na Kwanaki Uku

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

 

Hukumar Kula da Hasashen Yanayin Sararin Samaniya ta Kasa (NiMet) ta yi hasashen samun yanayin na rana da gajimare daga ranar Litinin zuwa Laraba a fadin kasar.

SOLACEBASE ta rawaito cewa Hasashen yanayin na NiMet da aka fitar ranar Lahadi a Abuja ya yi hasashen sararin samaniyar a yankin arewa a ranar Litinin a duk ranekun.

A cewarta, ana sa ran yanayin rana tare da gajimare a yankin Arewa ta Tsakiya a duk tsawon lokacin hasashen.

Advertisement

Hukumar ICPC fara sabon bincike kan yadda aka aiwatar da ayyukan mazabu 712 a fadin johohin kasar 20

” An yi hasashen yanayin iska mai tsananin da hasken rana a kan biranen Kudu da ke yakin kudanci tare da gajimare a yankin gabar teku da safe.

“Haka kuma, akwai yiwuwar samun tsawa a sassan Cross Rivers, Rivers, Bayelsa, Delta da kuma jihar Akwa Ibom,” in ji shi.

Ta yi hasashen yanayi mai hadari tare da hasken rana a yankin Arewa ta tsakiya a cikin lokacin hasashen.

Biranen da ke kudu da bakin teku ya kamata su kasance cikin gajimare tare da tsawa a sassan Rivers da jihar Cross River da safe.

“Washe gari ana sa ran tsawa a sassan Cross Rivers da Rivers da Bayelsa da Delta da kuma jihar Akwa Ibom,” inji ta.

Advertisement

Hukumar ta yi hasashen yanayi mara kyau a ranar Laraba tare da tazarar hasken rana a yankin arewa a duk tsawon lokacin hasashen.

A cewarta, ana sa ran yanayi mai hadari tare da hasken rana a yankin Arewa ta tsakiya a cikin lokacin hasashen.

Biranen da ke kudu da bakin teku ya kamata su kasance cikin gajimare tare da tsawa a wasu sassan Rivers, Akwa Ibom da jihar Cross River da safe.

“Washe gari ana sa ran tsawa a sassan Cross Rivers, Rivers, Bayelsa, Delta da Akwa Ibom.

“An shawarci ma’aikatan jirgin da su sami sabbin rahotannin yanayi daga hukumar NiMet don ingantaccen shiri a cikin ayyukansu,” in ji ta

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending