Connect with us

News

Hukumar EFCC ta kama wasu mutane 49 da ake zargi da damfara a Abuja

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

 

 

Jami’an rundunar shiyyar Abuja na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC sun kama wasu mutane 49 da ake zargi da damfarar yanar gizo. Wadanda ake zargin masu shekaru 19 da 32 ne, an kama su ne a wani samame da aka yi a gidaje daban-daban a rukunin gidajen ruwa da ke Cajaah-Orozo, a unguwar Abuja, biyo bayan samun bayanan sirri da ake zarginsu da aikatawa.

 

Advertisement

Daga cikin abubuwa da aka kama daga gare su sun haɗa da wayoyin hannu sama da hamsin , goma sha biyar da kuma mota lexus es330.

 

Za a gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu da zarar an kammala bincike.

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending