Connect with us

News

Yara biyu cikin biyar din da mahaifinsu ya cinna wa wuta sun mutu

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Ƴan sanda sun damke wasu abokai ƴan kungiyar matsafa dake tsafi da kawunan mutane a Ilori

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo ta bayyana cewa yara biyu cikin biyar din da mahaifinsu ya banka wa wuta sun mutu.

Advertisement

Ranar Alhamis Za A Yi Zaben Kananan Hukumomi A Neja

Kakakin rundunar Funmilayo Odunlami wacce ta sanar da haka wa PREMIUM TIMES ranar Talata ta ce yaran sun mutu a dalilin kunan da suka yi.

Advertisement

 

Funmilayo ta ce likitocin asibitin FMC Owo na kokarin ceto sauran yaran.

Advertisement

 

Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda mahaifin yaran mai shekara 54 Joseph Ojo ya cinna wa ‘ya’yan sa biyar wuta a gidan sa dake Fagun crescent a garin Ondo.

Advertisement

 

Sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna c Ojo ya duldula wa yaran fetur yayin da suke barci sannan ya kesta ashana.

Advertisement

 

Daya daga cikin yaran ya mutu a hanyar zuwa asibiti.

Advertisement

 

Wani da abin ya faru a idon sa da baya so a fadi sunnan sa ya ce Ojo ya aikata haka ne saboda rashin jituwan da ya ratsa tsakaninsa da matarsa.

Advertisement

 

Ya ce a wannan ranar Ojo ya so yin jima’i da matar sa amma sai ta ki bashi hadin kai kuma dama can ta dade tana kaurace masa.

Advertisement

 

Matar da Ojo ya aura bazawara ce da ta haifi ‘ya’ya biyar a aurenta na fari.

Advertisement

 

Bayan ta auri Ojo sai ta haifi ‘ya biyu wanda a yanzu haka sun kai wata 18 da haihuwa.

Advertisement

 

Funmilayo ta ce da zaran rundunar ta kammala gudanar da bincike za ta kai Ojo kotu domin yanke masa hukunci.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending