News
Sojoji sun kashe ƙasurgumin ɗan fashi a Kaduna
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Sojojin Najeriya sun ce sun kashe wani jagoran ƴan fashin daji a jihar Kaduna, mai suna Dogo Maikasuwa.
Wata sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar, Samuel Aruwan ya fitar, ranar Juma’a, ta ce an hallaka Maikasuwa ne lokacin da dakarun suke sintiri a ƙaramar hukumar Chikun.
An kama mutum 600 a Chadi saboda ‘shiga zanga-zanga’
Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun samu nasarar ƙwato bindiga ɗaya ƙirar AK-47, da alburusai, da babura biyu da kuma kayan sojoji.
Ta ƙara da cewar Dogo Maikasuwa, wanda ake kira da Maimillion ya jagoranci kai hare-hare da garkuwa da mutane masu bin hanyar Kaduna zuwa Kachia da kuma wasu kauyuka na ƙaramar hukumar Chikun.
Advertisements
