News
Ƙasar Amurka ta ware Dala miliyan 50 saboda zaɓen Najeriya
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ƙasar Amurka ta ware Dala miliyan 50 domin tallafa wa Najeriya gudanar da zaɓen shugaban kasa a shekara mai zuwa.
Daga cikin abubuwan da za a yi da kudaden har da horas da ‘yan jarida da kungiyoyin fararen hula baya ga taimakawa wajen samar da kayayyakin aiki domin tabbatar da ingantaccen zabe.
Air Peace Ya Dakatar Da Jigilar Zuwa Dubai Saboda Hana ‘Yan Najeriya Biza
Jakadan Amurka, Mista Will Stevens, shi ne ya sanar da tallafin a wannan Litinin a birnin Ibadan, babban birnin jihar Oyo a yayin wani taron horas da ‘yan jarida wanda Cibiyar Horas da Yada Labarai ta Yammacin Afrika WABMA ta shirya.
Mista Stevens ya ce, gwamnatin Amurka na aiki tukuru da aminanta ta hannun Hukumarta ta Raya Kasashe Masu Tasowa USIAD, domin ganin an kidaya kuri’ar kowa da kowa a yayiin zaben na 2023 a Najeriya.
