News
ASUU za ta ware ranar da ba za ta shiga aji ba
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya ta ce za ta ayyana ranar da ba za ta shiga aji ba a jami’o’in ƙasar domin bayyana rashin jin daɗinsu game da zargin da take yi wa gwamnatin tarayya na riƙe musu albashin wasu watanni.
Najeriya na da isassun kudaden da za ta kula da kowane dan kasa. – Kwankwaso
Babban jami’in ƙungiyar mai lura da shiyyar Kano Farfesa Abdulkadir Muhammad ya shaida wa BBC cewa ƙungiyar ASUU ta yanke shawarar ne domin bayyana ɓacin ranta kan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na ƙin biyan mambobin ƙungiyar albashinsu na wasu watanni bayan sun janye yajin aiki.
Ya ce ”kowane reshe zai zaɓi rana guda da zai gudanar da taro tare da zanga-zangar lumana, domin nuna ɓacin ransu da rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnatin tarayya ke ƙoƙarin mayar da malaman jami’o’i ma’aikatan wucin gadi”.
Ya ƙara da cewa ”ASUU za ta gudanar da taro a kowane reshe na ƙungiyar, inda kuma duka mambobin ƙungiyar za su hallara, bayan gabatar da laccoci a wajen taron, mambobin ƙungiyar za su gudanar da zanga-zangar lumana a cikin kowacce jami’a, sannan kuma a ranar ba za su shiga aji domin koyawa dalibai karatu ba’
A cikin watan Oktoba ne ASUU ta janye yajin aikin da ta kwashe wata takwas tana gudanarwa.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
