News
Samar da makamin nukiliya mafi girma a duniya ne burinmu – Kim Jong-un
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ya ce aniyar ƙasarsa ita ce samar da makamin nukiliya mafi girma a duniya.
Yan sanda sun kama matashi kan zargin yi wa yaro fyade har ya mutu
Mista Kim ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da kafar yaɗa labaran ƙasar, a daidai lokacin da yake bayani kan ƙaddamar da makamin nukiliya da na linzami masu cin dogon zongo da ƙasar ta ƙera a farkon watan nan.
Ya kuma raɗa wa makamin suna da ‘Gwarzon ƙasa’ haka kuma ya nuna tare da tabbatar da ƙarfin ƙasar a wannan fanni.
Kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya dai ya haramta gwajin irin wannan makamin, kuma Amurka ta buƙaci Koriya ta Arewan da ta sauya matsayinta kan wannan, sannan kuma ta jira abin da zai biyo baya.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
