Connect with us

News

Yan sanda sun kama matashi kan zargin yi wa yaro fyade har ya mutu

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun da ke kudpu maso yammacin Najeriya ta ce ta kama wani matashi da take zargi da yi wa wani ƙaramin yaro mai shekara biyar fyade, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar yaron.

Advertisement

An yanke wa mutumin da aka kama da katin zaɓe 101 hukuncin shekara ɗaya

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Abimbola Oyeyemi ya sanya wa hannu ya ce an kama matashin mai shekara 36 bayan da shugaban ƙungiyar ci gaban al’umar yankin ya kai ƙorafin matashi zuwa ofishin ‘yan sanda.

“Bayan samun rahoton sai shugaban ‘yan sanda na ofishin ya yi gaggawar tura jami’an tsaro inda nan take suka kamo wanda ake zargin”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Advertisement

“A yayin da aka tuhumi wanda ake zargin ya tabbatar wa da ‘yan sanda cewa shi mai neman maza ne dalilin da ya sa kenan ya haike wa yaron”.

Tuni dai kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bayar da umarnin mayar da batun sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar domin faɗada bincike.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending