Connect with us

News

NNPP: ‘Ba za mu sa hannu kan shirin zaman lafiya lokacin zabe a Kano ba’

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Jam’iyyar adawa ta NNPP da ɗan takararta na gwamna a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, sun yi barazanar ƙauracewa sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya don tabbatar da ganin an gudanar zaɓuka cikin kwanciyar hankali da lumana.

Advertisement

Gwamnatin jihar Kano ta haramta wa Yan Adaidaita Sahun bin manyan Titunan jihar Kano

Shugaban jam’iyyar a Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya shaida wa BBC cewa, su a tsarinsu ba zasu je su sanya hannu a kan abin da suka san cewa idan aka tabasu ba zasu kyale ba.

Ya ce, an yi irin haka ba sau daya ba to a yanzu sun kai makura.

Advertisement

Shugaban na NNPP a Kano, ya ce ko baya bayan nan shugaban APCn, Abdullahi Abbas sai da ya ce koda tsiya-tsiyar sai sun ci zabe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending