News
Tsohon Shugaban China, Jiang Zemin, Ya Rasu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rahotanni daga kasar China sun ce tsohon Shugaban Kasar, Jiang Zemin, ya rasu.
Jiang ya rasu ne a Shanghai ranar Laraba, inda ya bar duniya yana da shekara 96.
Sanarwar rasuwar marigayin na kunshe ne cikin wata wasikar hadin gwiwa tsakanin hukumomin kasar da kuma babbar jam’iyyar kasar suka fitar.
Wasikar ta nuna yadda dukkan wadanda wasikar ta shafa suka mika ta’aziyyarsu ga al’ummar China dangane da rasuwar tsohon Shugaban.
Kazalika, wasikar ta nuna marigayin a halin rayuwarsa, shugaba ne tsayayye kuma mai kima a idon duniya wanda ya kasance abin so ga daukacin al’ummar kasar.
Ta kuma bayyana matuwarsa a matsayin babban rashi ga kasar baki daya.
(NAN)
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
