Connect with us

News

Ƙungiyar ƙwadago ta bayyana damuwarta kan ƙaranci man fetur a Najeriya

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Haɗakar ƙungiyoyin ƙwadago ta Najeriya ta bayyana damuwarta game da ƙarancin man fetur da ƙaruwar farashinsa a faɗin ƙasar.

 

Advertisement

A wata sanarwar haɗin gwiwwa da ƙungiyoyin NLC da TUC suka fitar, sun ce ba su ga dalilin da zai sa a samu ƙarancin fan a fadin ƙasar ba, saboda a cewarsu gwamnati ce kaɗai ke da alhakin shigo da man cikin ƙasar.

Burkina Faso ta dakatar da rediyon RFI yaɗa shirye-shirye a ƙasar

Dan haka a cewarsu ba su ga dalilin da zai sa wata hukuma ta gwamnati za ta ƙara kuɗin da take sayar wa ‘yan kasuwa ba

 

Sanarwar ta ƙara da cewa ƙungiyoyin sun samu wata masaniya da ke nuna cewa da gayya aka ƙirƙiri matsalar domin a riƙa sayar da man sama da farashin da gwamnati ta amince da shi.

 

ƙungiyoyin ƙwadagon sun umarci gwamnati da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar kafin abubuwa su lalace.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending