News
Ya Yi Bidiyon Tsiraici Don Name Wa Tinubu Nasara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitaccen jurmin fina-finan Najeriya, Ebun Oloyede, wanda aka fi sani da Olaiya Igwe ya yi wa kansa tsirara, haihuwar uwarsa, don roka wa dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar APC, Bola Tinubu, nasara a zaben 2023.
Fitatccen jarumin kuma mai shirya fim din, ya wallafa bidiyonsa yadda ya yi zindir a bakin teku yana rokon dodon teku cikin harshen Yarbanci ya ba wa dan takarar sa’a.
Netherlands ta tsallaka mataki na gaba bayan doke Amurka da ci 3-1 a Qatar
“Ya ubangini na zo gare ka ne saboda Bola Ahmed Tinubu; ina rokon ka ka ba shi nasara a zabe mai zuwa,” in ji Olaiya Igwe, a cikin bidiyon da ake ganin wani sabon salo ne na yakin neman zabe.
Tuni dai bidiyon nasa da ya wallafa a shafin na Instagram ranar Juma’a ya karade kafofin sada zumunta, inda masu tsokaci su ka yi masa ca a martaninsu kan bidiyon nasa.
An ji shi a ciki yana cewa, “Na zo bakin teku ne musamman domin in roke ka, ka sa yawan kuri’un da Tinubu zai samu su yi yawa kan ruwan teku, kada ka bari mu ji kunya.”
