News
Kwankwasiyya ta Nada Muhuyi Magaji A Matsayin Daraktan Leken Asiri Da Dabaru
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Majalisar yakin neman zaben Kwankwasiyya ta amince da nadin tsohon shugaban hukumar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci da rashawa ta Kano Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin daraktan leken asiri da dabaru na majalisar yakin neman zaben.
Sunusi Bature Dawakin Tofa, Kakakin Majalisar Yakin Neman Zaben Gwamna na NNPP necya bayyana haka.
Muhuyi Magaji yana takun saka tsakaninsa da gwamnatin jihar Kano a yanzu karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje tun bayan da majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shi a matsayin shugaban hukumar a watan Yulin 2021.
Advertisements
