News
Babu laifin mu a wahalar man fetur da a ke yi a Nijeriya – IPMAN
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ƙungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN, ta fitar ce ba laifinta ba ne a ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar.
Ƙungiyar ta kuma ce mambobinta ba su da hannu a ƙarancin da ake fama da shi a halin yanzu.Femi Adelaja, Shugaban IPMAN ta defot ɗin Mosinmi a Jihar Ogun, a wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, ya ce babu man fetur a cikin gidajen man fetur na ƙasa (NNPC) a faɗin Nijeriya.
Ya ce a yanzu haka farashin man fetur daga defot ya kai Naira 220 a faɗin gidajen man da ke Legas.A cewarsa, ‘yan kasuwan sun koma siyan kayan ne daga defot-defot na masu zaman kansu, inda suke sayar da kayan a farashi mai tsada.
Don haka ya danganta matsalar ƙarancin man da ake fama da ita a halin yanzu ga gwamnatin tarayya da kuma gazawar kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) wajen samar da man ga mambobinsa a farashi mai sauƙi.
-
News6 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi
-
News6 days agoDSS Ta Gurfanar Da Mutum Biyar Gaban Kotu Bisa Zarginsu Da Garkuwa Da ‘Yan NYSC 20 A Imo

