Connect with us

News

Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

 

 

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), ta tabbatar wa al’ummar Nijeriya cewa, ba a ajiye na’urorin tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) a wuraren da ‘yan bangar siyasa su ka kai hari tare da ƙona su kwanan nan ba.

 

Advertisement

INEC ta kuma ce wasu muhimman kayyakin da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaɓukan 2023 su na nan lafiya ƙalau cikin tsaro.

Babu laifin mu a wahalar man fetur da a ke yi a Nijeriya – IPMAN

 

Kwamishinan INEC na Ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan jama’a da wayar da kan masu kaɗa ƙuri’a, Mista Festus Okoye ne ya sanar da hakan a wani shiri na gidan Talabijin na Channels a Lahadin da ta gabata.

Okoye ya sake nanata cewa za a gudanar da babban zaɓen ƙasar na shekara mai zuwa duk da hare-haren da aka kai wa ofisoshinta.

 

Jaridar blueprint ta rawaito cewa Hukumar zaɓen ƙasar ta koka kan yawaitar hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa, inda adadin ofisoshin da abin ya shafa ya kai 50, a faɗin jihohi 21.

Advertisement

 

 

Sai dai yayin da yake magana a jiya, Okoye, ya ce muhimman kayan da za a tura domin zaɓen baɗi ba sa cikin wuraren da aka kai harin kwanan nan.

 

“Ina so in tabbatar wa al’umma cewa kayanmu masu mahimmanci ba sa cikin waɗannan wuraren da waɗannan hare-haren suka faru.

 

Advertisement

“Mun tabbatar da tsaron tantance masu kaɗa ƙuri’a (BVAS) da sauran wasu muhimman abubuwa da za a yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen.

 

 

”Waɗannan kayan ba sa cikin waɗannan wuraren da ake kai wa hari,” inji Okoye.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending