News
Kotu Ta Tsare Matashi A Kurkuku Kan Zargin Fyade
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wata kotu a Jihar Kaduna ta ba da umarnin tsare matashi gidan gyaran hali kan zargin yi wa ’yar shekara 14 fyade.
Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Chidi Leo, ya fada wa kotun ranar Alhamis cewa, wanda ake ya tafi shagon su yarinyar ce ya yi sayayya sannan ya bukaci ta bi shi ta karbi kudi ganin cewa makwabta suke.
Na’urorin BVAS da sauran muhimman kayan zaɓe na nan lafiya ƙalau — INEC
Ya ce, da isarsu, “Sai ya kama kofar dakinsa ya rufe sannan ya yi mata fyade.”
Lamarin da ya ce ya auku a ranar 30 ga Nuwamba.
Alkalin kotun, Ibrahim Emmanuel, ya ki amincewa da rokon da matashin ya yi wa kotun, inda ya ba da umarnin a kai shi kurkuku sannan ya dage shari’ar zuwa Janairu.
(NAN).
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
