News
Kotun Amurka na tuhumar ɗan Mauritania da kisan Turawa a Mali
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Wata kotu a birnin New York na Amurka na tuhumar wani mutum ɗan ƙasar Mauritania da laifukan ta’addanci da ke da alaƙa da wasu hare-hare da ya kai kan Turawan Yamma a ƙasar Mali a 2015.
Mutum 38 aka kashe a harin, ɗaya daga cikinsu Ba’Amurke ne.
Kwamitin Gudaji Kazaure haramtacce ne, ba Shugaba Buhari ya kafa shi ba – Garba Shehu
An gurfanar da Fawaz Ould Ahmed kwana ɗaya bayan da aka tasa ƙeyarsa daga Mali inda a nan ma aka yanke masa hukuncin kisa bayan amincewa da laifinsa.
Ya shaida wa kotu a Mali cewa ya kai harin ne domin ɗaukar fansa kan zanen ɓatanci da mujallar nan ta Charlie Hebdo ta yi kan Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam.
BBC ta rawaito cewarsa, ko kaɗan ba ya nadama kan irin hare-hare da ya kai a wuraren shan barasa da otel-otel waɗanda baƙin Turawa kan sauka a Mali.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
