News
Yadda Dogayen Layi ke karuwa A Gidajen Mai A Kano duk da Umarnin da DSS ta bayar ga NNPC
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Duk da bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga Kamfanin Man Fetur na Kasa NNPC, da kuma ‘yan kasuwar mai da hukumar tsaron farin kaya DSS, na su gaggauta magance matsalar karancin man abu ya ci tura.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Alhamis ne hukumar DSS ta bai wa kamfanin mai na NNPC da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma wa’adin sa’o’i 48 da su kawo karshen matsalar karancin mai a fadin kasar nan.
Jami’in hulda da jama’a na DSS, Peter Afunanya, wanda ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, ya bayyana cewa wa’adin ya zo ne bayan da hukumar ta yi wata ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkar man fetur, inda suka amince a kawo karshen karancin man a cikin lokacin da aka kayyade.
Sai dai masu sayar da man a ranar Juma’a, sun ce har yanzu ana samun matsala wajen rabon sa, amma sun bayyana kwarin gwiwarsu na ganin nan ba da jimawa ba layukan sayar da man a gidajen mai daban-daban za su zo karshe.
A jihar Kano ma lamarin ƙara ƙamari yake, saboda yadda ake ci gaba da samun dogayen layuka a gidajen Man dake siyarwa akan farashin gwamnati.
Yayin da na yan kasuwa farashin Litar ya kai Naira 310, duk da cewa shima wannan sai an sha wahala ake iya samun sa.
Wani mai tuka babur din A-Daidaita-Sahu, Shuaibu Ibrahim, ya shaida wa jaridar indaranka cewa ya shafe kimanin awa uku a kan layi kafin ya samu mai.
