News
Babu hannuna a kisan kiyashin 2009 – Moussa Dadis Camara
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon shugaban mulkin soja na Guinea Moussa Dadis Camara, ya musanta hannunsa a kisan kiyashin da jami’an tsaro suka yi a shekara ta 2009.
Ana tuhumar sa tare da wasu tsoffin jami’an soji da na gwamnati 10 kan kisan mutane sama da dari da hamsin da kuma yi wa mata fiye da dari fyade.
Mutum uku sun mutu bayan ‘yan bindiga sun kai hari a ofishin INEC da ke Imo
Hakan ya faru ne a cikin wani filin wasan kwallon kafa inda ‘yan adawa ke kokarin gudanar da gangamin siyasa.
Ana tuhumar Mista Camara ne da laifin daukar nauyin wadanda suka aikata mummunan laifin.
An soma shari’ar kisan kiyashin a watan Satumba, kuma bayyanar Camara wani muhimmin abu ne ga wadanda suka tsira da rayukansu da kuma dangin wadanda aka kashe
