Connect with us

News

Likitocin Da Suka Samu Horo A Kasashen Waje 439 Sun Fadi Jarabawar Gwaji

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Hukumar kula da aikin likita ta kasa, ta ce likitocin da su ka samu horo daga kasashen waje akalla 439 ne su ka fadi jarabawar gwajin da za ta ba su damar yin aiki a Nijeriya.

Advertisement

 

Shugaban hukumar Dr Tijjani Sanusi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai, inda ya ce likitocin da su ka samu horo daga kasashen waje 916 ne su ka zana jarabawar, amma 477 ne kawai su ka ci.

Advertisement

Najeriya Ta Kirkiro Rigakafin Cutar Sikila

Ya ce ana gudanar da irin wannan jarabawar ko ina a fadin duniya, kuma babu wani kwararren da za a bari ya yi aiki a kasar da ba a nan ya yi karatu ba sai idan ya ci jarabawar.

 

Advertisement

An dai gudanar da jarabawar gwajin ne a asibitin koyarwa na jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, domin tabbatar da cewa duk likitan da ya yi karatu a wata kasa ya nuna kan sa a matsayin wanda zai iya gudanar da aikin sa a Nijeriya.

 

Advertisement

Da wannan lasisin ne, wadanda su ka karanci aikin likita a kowane fannni za su yi aikin wucin-gadi tsawon shekara guda, daga nan ne za a ba su cikakken lasisi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending