Connect with us

News

Sai an biya mu naira miliyan 100 za mu sako daliban matan kwalejin Yauri – Gide

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Fitaccen ‘dan ta’addan jihar Zamfara Dogo Gide da yayi garkuwa da dalibai mata ‘yan kwalejin Yauri dake jihar Kebbi ya rantse ba zai saki sauran wadanda suka rage a hannunsa tare da malaman sub a har sai an kai masa diyyar naira miliyan 100 da ya bukata.

Advertisement

 

Liberty kano ta rawaito cewa Wannan matsayi ya biyo bayan wani sautin hirar da aka nada tsakanin wani daga cikin mahaifin dalibar dake hannunsa da mahaifiyarsa wadda ta bukaci ya sake sauran wadanda yayi garkuwar da su.

Advertisement

Jagaba Tinubu ya ziyarci Birnin-Gwari kafin fara yakin neman zabensa a Kaduna

Gide wanda yayi kaurin suna wajen kai munanan hare hare yana hallaka jama’a a Jihohin Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna, yace muddin iyayen daliban na bukatar ganin sun kubuta, toh dole sai sun biya wadanan kudade da ya gindaya.

 

Advertisement

Sautin da aka nada ya bayyana wata mata da akace itace mahaifiyar ‘dan ta’addan tana nuna damuwa akan ci gaba da garkuwa da daliban, musamman ganin kananan yara ne.

 

Advertisement

Mahaifiyar ta bayyana cewar bata zama da ‘dan nata a daji, amma ta ziyarce shi ne a wannan karo, kuma ba zata bar wurin da yake ba har sai an kammala tattaunawa tsakanin sa da iyayen daliban da aka tsare da su domin ganin sun kubuta.

 

Advertisement

An jiyo mahaifiyar dan ta’addan na cewa jama’a suyi hakuri da ‘dan nata saboda yaranta ne ke dibarsu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending