Connect with us

News

Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna Ya Murkushe Wata A Mota

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

Jirgin fasinja da ke tafiya daga Abuja zuwa Kaduna ya murkushe wata mata a mota har lahira a unguwar Kubwa da ke Abuja a jiya Alhamis.

Advertisement

 

Rahotanni sun ce matar na kokarin tsallaka titin jirgin kasar ne da motarta, yayin da jirgin ke daf da ita, inda yai ciki da ita da misalin karfe 10:00 na safe.

Advertisement

NAFDAC Ta Kwace Jabun Magunguna Na N20m A Kasuwar Zariya

Mai magana da yawun hukumar kula da layin dogo ta Najeriya (NRC), Mahmood Yakoob, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin amma bai bayar da cikakken bayani.

 

Advertisement

Wani faifan bidiyo na wannan mummunan lamari da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna cewa jirgin ya murkushe wata bakar mota kirar Toyota Camry daga bangaren direban yayin da motar ke tsallaka titin jirgin, a jiya Alhamis.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending