Sports
Shin Benzama zai bugawa Faransa wasan karshe a Qatar?
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Yayin da ake saran karawa tsakanin Faransa da Argentina a wasan karshe na cin kofin duniya, yanzu haka ana ci gaba da rade radin cewar ‘dan wasan gaba na kungiyar Real Madrid Karim Benzema na iya shiga cikin tawagar wadanda zasu takawa Faransa wasa a karshen mako.
Kafofin yada labarai da dama sun ce Benzema ya warke daga raunin da yake samu, kuma har ya fara atisaye da kungiyarsa ta Madrid inda yake ci gaba da samun horo domin dawo da karsashinsa da aka san shi akai.
Sai dai mai horar da ‘yan wasan Faransa Didier Deschamp yayi watsi da irin wannan tambayar da aka masa cewar Benzema zai shiga cikin tawagar da za su yiwa kasar wasa a ranar lahadi.
Deschamp ya bayyana tambayar akan komawar Benzema a matsayin rashin hankali, saboda halin da yake ciki da kuma yadda ya fice daga cikin tawagar Faransa saboda raunin da ya samu.
Manajan yace Benzema bai koma akan karsashin da aka san shi ba, saboda haka babu dalilin danganta shi da komawa cikin tawagar ‘yan wasan duk da yake suna girmama shi saboda gudumawar da ya baiwa Faransa.
Yanzu haka dai hakkin jagorancin tawagar Faransa a fili ya rataya akan Olivier Giroud da Kylian Mbappe da kuma Antoine Griezmann.
Fri
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
