Business
Gwamnatin Najeriya na fatan haɓaka hada-hadar cikin ƙasa zuwa dala tiriliyan 12
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin Najeriya ta ce tana fatan cimma dala tiriliyan 12 a matsayin darajar dukiyar da ake samarwa a cikin ƙasar (GDP) da kuma dukiyar da ‘yan ƙasar ke samu nan da 2050.
Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta faɗa ranar Juma’a a Abuja cewa an yi hasashen cimma wannan adadi ne idan adadin dukiyar Najeriyar ta cikin gida ya ci gaba da haɓaka da kashi 7 cikin 100.
“Za a iya cimma wannan adadi mai girman gaske ne kawai idan masu ruwa da tsaki suka ƙirkiri hanyoyin koyarwa ingantattu a faɗin Najeriya ta hanyar zuba jari kamar yadda aka tsara a Tsari na Ƙasa,” in ji ta.
Da yake tana magana ne a wurin taron neman hanyoyin kafa cibiyoyin ilimi masu ƙwari, ministar ta ce gwamnati ta fara wani shiri na gina makarantu ta hanyar haɗin gwiwa da EEG a 2021 da zimmar kare makarantun daga hare-haren ‘yan bindiga.
Ta ce yunƙurin ya sa an fito da “Tsari na Ƙasa”, wanda ake sa ran aiwatarwa tsakanin 2023 da 2026 da kuɗi naira biliyan 144.8.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
